Kasashen Turai sun dauki tsawon lokaci suna nazari kan wannan sabon tsarin kasuwancin da Iran wanda ya kunshi cinikayya tsakanin bangarorin biyu amma ba da takardun kudin Dala ba.
Koda yake akwai yiwuwar sabon tsarin ba zai fara aiki gadan-gadan ba har sai bayan wasu watanni sakamakon wasu bayanai da ake dakon su.
Manyan kasashen duniya da ke kawance da Amurka sun nuna adawarsu da matakin da shugaba Donald Trump ya dauka na watsi da yarjejeniyar nukiliyar Iran wadda a sanadiyar ce aka dage wa kasar takunkuman karayar tattalin arziki.
Daga bisani Iran ta yi barazanar yanjewa daga wanann yarjejeniya har sai manyan kasashen Turai sun samar ma ta da kafar samun alfanun tattalin arziki, kuma tuni kasashen suka yi alkawarin tallafa wa kamfanoni wajen yin harkokin kasuwanci da Iran muddin kasar ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar.